29 Nuwamba 2020 - 15:23
Sojojin Kasar Habasha Sun Shiga Babban Birnin Gundumar Tigray

Pira ministan kasar Habahsa Abiy Ahmad ne ya sanar da cewa sojojin kasar sun shiga birnin mekelle da marecen jiya Asabar wanda shi ne babban birnin gundumar Tigray

ABNA24 : Pira minista Abiy Ahmad ya kara da cewa; Hadin kan da mutanen birnin su ka bai wa sojojin tarayyar kasar ne ya taimaka wajen samun nasara cikin gaggawa.

Bugu da kari Pira minstan kasar ta Habasha ya ce; sojojin tarayyar kasar sun girmama mazauna birnin na Mekelle, sannan kuma ya yi alkawalin sake dawo da rayuwa ba da jimawa ba.

A farkon wannan watan ne na Nuwamba yaki ya barke a tsakanin sojojin tarayyar Habasha da kuma na yankin Tigray da ke son ballewa daga kasar.

342/